Yadda Sabon Tsarin Rajista JAMB Yakawo Sauyin Kura Kurai Da Dalibai keyi Yayin Rajista

Ada kafin fara sabon tsarin rijista jarabawar JAMB, dalibai da dama sun kasance suna samun kansu cikin aikata kurarai da suka hada da rubata suna , adreshin Email, shekarun haihuwa, karamar hukuma da sauran su ba daidai ba.

Wannan kura kurai ya dade yana Kai kawo tsakanin dalibai a dukan shekara lokacin rijista jarabawar JAMB, sai dai saukin abun ana iya gyara wadanan kura kuran ama ba kyauta ba, sai an biyan wanni sabon kudin.

NOMBAR NIN

Ama zuwan wannan sabon tsarin rijista jarabawar JAMB tare da numbobin katin dan kasa wato (NIN), ya magance wa dalibai wadanan matsaloli, domin kuwa dazarar an saka nombobin katin dalibai ta NIN dukan Jerin bayanan daliban zai fito.

ba tare da an bukaci daliban subayar ba kamar da, hakan yataimaka matuka gun kawar da batun kura kurai, saidai in dama chan dalibi ya yi kuskure lokacin da yake rijista katin dan kasa.

Zamu iya cewa wanna tsari ba karamar nasara bane tare da cigaba da saurin gun rijista jarabawar da Hukumar Jarabawar JAMB ta kawo wa dalibai.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*