Shin Ko Rashin Daura Sakamakon Olevel A Shafin JAMB Caps Na da Illa Ga Dalibai?

Tunbaya da Hukumar Jarabawar sharan fagen shiga makaratu ga ba da sakandiri a Nijeriya, JAMB ta karba ragamar bada guraben karatu ga dalibai, aka samu sauye sauye da dama Daya hada da fitowar JAMB Caps.

JAMB

Mene ne JAMB CAPS?

Shi dai JAMB Caps wani shafi ne da Hukumar Jarabawar JAMB ta kirkira don kula da ba da guraben karatu. Shafin a shirya shi kuma dabashi umarni baiwa dalibai gurbin karatu in suka cike wasu ka idoji da aka gindaya cika harda daura sakamakon Jarabawar Olevel (WAEC, NECO, NABTEB, NBAIS) tare da sakamakon OND, NCE, IJMB, HND ga masu neman gurbin Direct Entry.

Duba da yadda aka tsara da bada umarni ga shafin JAMB CAPs, dalibai da basu daura sakamakon Jarabawar Olevel dinsu ba kan fuskaci illar Rashin samun gurbin karatu a shekarar da yanema sabanin da da tun alokacin yin rigista ne ake da bukatar dalibai su saka bayanan jarabawar Olevel din su.

Yazama dole ga duk daliban da suke bukatar samun gurbin karatu a kowace makaratar indai sharadin neman makaratar ya hadda da sai anyi jarabawar JAMB su daura sakamakon Jarabawar Olevel din su a shafin JAMB CAPs.

Yaya Dalibai Zasu Daura Sakamakon Jarabawar Olevel a Shafin JAMB CAPs?

Hanya dayace dalibai zasu bi don daura sakamakon Jarabawar Olevel dinsu a shafin JAMB CAPs, shine ta hanyar ziyartan cibiyoyin rijista jarabawar JAMB da Hukumar ta basu lasisi aiwatar da hakan don a daura musu sakamakon Jarabawar Olevel dinsu.

Cibiyoyin ne kadai akayi wa izini yin wanan aiki bayan su ba za’a iya daurawa ba ako ina bah,da dama dalibai Kan kai wa masu cyber cafe don ayi musu ama bayayi sai dai sukarbi kudin su.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*