Shin Ko Rashin Hadakar Darusu Da Yadace Gurin Rijista JAMB Nada Illa Ga Dalibai ?

Kowani kwas da Dalibai ke bukatar karanta na da kalar Hadakar darusa da ake bukata domin yayi daidai da shi, a fadin makaratun Nijeriya.

A kowace shekara Hukumar gudanar da Jarabawar sharan fagen shiga makaratu ga ba da sakandiri wato JAMB, na fitar da manhajar hadakar da za ayi anfani dashi na kowane kwas ga dalibai.

Sai dai dalibai da dama basu bibiya ko kuma bincike wadanan hadaka darusa don duba ko ya dace da kwas din da zasu karanta a makaratun gaba da sakandire.

Dalibai da dama na zaban darusan da suka fi kwarewa ne akai don su samu maki mafiyawa bayan Kamala Jarabawar sharan fagen shiga makaratu ga ba da sakandire, wasu Kuma Kan baiwa masu rijista jarabawar damar musu zabi darusan daya dace.

Hakan na matukar illatar da Dalibai musaman bayan sun Samu gurbin karatu a makaratun da suke da muradi, domin ko makaratu da dama na daukar matakai tsatsaura akan wanan matsalar akan dalibai.

Inma dai ko dalibi ya rasa gurbin karatun gaba daya ko kuma makaratar ta sauya wa dalibi kwas din da zai karanta, hakan na faruwa da dalibai da dama a Nijeriya.

JAMB

Hanyoyin Da Dalibai Zasu bi don guje wa matsalar hadakan darusa yayin Rijista JAMB ?

Dalibai yakamata su karanta manhaja Jarabawar JAMB na shekara shekara wato (JAMB SYLLABUS) a turance, don sannin Hadakar darusa da yadace da kwasakwasan da suke da burin karantawa a Fadin makaratun Nijeriya.

Hanya ta biyu shine dalibai su ziyarci shafin makaratun da suke da bukatar yin karatu na intanet don bin cikar Hadakar darusa da Jami’ar ta ware wa kowani kwasakwasan da take gudunarwa.

Dalibai Zasu aiwatar da wanna matakai ne kafin suje gun rijista jarabawar JAMB din ko Kan sunyi.
Domin kuwa ba achanja zababen darasu bayan an Kamala rijista jarabawar JAMB.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*