NAUB : Ta Fara Saida fom Din Post UTME/DE na shekarar 2020/2021

Hukumar Jami’ar Nijeriya Army dake biu a Jihar Borno (NAUB), Ta far Saida form din neman gurbin karatu wato post UTME/DE na Zangon karatun shekarar 2020/2021.

Anagayatar dalibai da suka chanchan ta don cike wanan gurbin na karatun digirin Farko na tsawon shekara hudu a Jami’ar Nijeriya Army Biu.

Fom din zai dauki kwana Sha uku ne kacal ana siyar dashi, za afara Saida fom din NAUB 2020 Post UTME/DE daga ranar 30 ga watan Afrilu, 2021 zuwa ranar 13 ga watan mayu, shekara 2021.

Dalibai dasu ka chanchanci cike gurbin karatu a Jami’ar NAUB post UTME/ DE 2020.

Dukan daliban da suka zabi Jami’ar a zabin Farko na jarabawar JAMB 2020, sanan suka ci maki 180 sai masu Matakin karatu Difloma kada yayi kasa da Upper credit NCE Kuma 12point ne zasu iya cike fom din.

Bugu da kari dolene dalibai su kasance suna da credit 5 a sakamakon Jarabawar Olevel dinsu cike harda darasin turanci da lisafi, kada ya wuce a zana Jarabawa biyu.

Hanyar Da Dalibai zasu bi gun cike gurbin fom din post UTME/DE na Jami’ar NAUB na shekarar 2020/2021.

Dukan dalibai da zasu ne ma gurbin karatu a Matakin UTME /DE zasu biya naira 2000 a matsayinta kudin fom din tantancewa a shafin Remita. Sanan dalibai su tabatar sun daura sakamakon Jarabawar Olevel dinsu a shafin JAMB CAPs.

Bugu da kari dalibai da zasu ne ma gurbin karatun DE su tura sakamakon Kamala karatun A level dinsu a adreshin Email din :admission@naub.edu.ng.

Yadda Dalibai zasu biya kudin NAUB 2020/2021 Post UTME/ DE.

  • Dalibai su ziyarci shafin ramita akan adreshi www.remita.net .
  • Su bincika Jami’ar Nijeriya Army Biu amatsayin Wanda zasu biya.
  • Su zaba biyan kudin tantacewar gurbin karatu, su cike dukan ababen da ake bukata sai su sa #2000.
  • Zu zaba hanyar biya kudin ko ta banki ko kuma da katin cire kudi.
  • Bayan biyan kudin dalibai zasu tura Takarda shaidar biyan kudin tantacewar a adreshin Email din admission@naub.edu.ng.
  • Dukan daliban da aka tabatar da biyan kudin sune za abawa gurbin karatu.

Kusani: dukan matakai Nan za agamasu ne kafin ko kuma ranar 13 gawatan mayu, shekara 2021.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*