UMYU: Zata Gudanar Da Jarabawar post UTME/DE Shekarar 2020/2021 A Karo Na Biyu

Rijistaran Jami’ar Umaru Musa Yar’adua dake Jihar Katsina, Malam Nasiru Bello, na sheda wa daliban da suka chanchanci samun gurbin karatu a Jami’ar, masu maki 170 zawa sama a jarabawar JAMB kuma Wanda suka yi rijista gurbi karatu post UTME/DE Jami’ar cewa za a gudanar da Jarabawar tantace gurbin karatu a Karo Na Biyu a ranar 22 gawatan mayu, 2021.

Dalibai dasuka cika fom din post UTME DE da basu samu damar halarta jarabwar a Karon farko, toh dama yasamu musu don zuwa akarao na biyu.

Haka zalika, daliban da suka zaba Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, sanan Basu samu damar cike fom din post UTME/DE suma zasu iya halartan jarabawar a Karo Na Biyu.

Sanan daliban dake burin chanja zabin farkon su zuwa Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, nada damar sauyawa a cibiyoyin rijista jarabawar JAMB, sanan su yi rijista fom din post UTME/DE akaro na biyu don halartan jarabawar.

Dole ne dalibai su tabatar sun da credit 5 a sakamakon Jarabawar Olevel dinsu ciki harda darasin turanci da lisafi.

Ana bukatar Daliban dazasu zo zana Jarabawa su zo da takarda shedan rijista jarabawar JAMB me dauke da hoton su, Jami’ar a matsayin zabin Farko da kwas din dasuke nema.

Daliban zasu hado da sakamakon Jarabawar Olevel dinsu Wanda zasu rubuta numba rajista JAMB dinsu babba asamar sa, sanan zasu bayar da kofin sa lokacin shiga zana Jarabawa.

Dole ne dalibai su kiyaye da matakan kariya daga yaduwar annobar corona wato Covid-19.

Don Karin bayani dalibai su ziyarci shafin Jami’ar Umaru Musa Yar’adua.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*