FUWUKARI: Ta Sake Guraben Karatu Shekarar 2020/2021, a Shafin JAMB CAPs

Jami’ar Gwamnatin Taraya ta Wukari (FUWUKARI), ta saki guraben karatu na shekarar 2020/2021 a Shafin intanet na JAMB CAPs.

Ana farincikin sanar da daliban da suka ne ma guraben karatu a Jami’ar FUWUKARI da su garzaya shafin intanet na JAMB CAPs don duba ko sun sama guraben karatu a Jami’ar.

Dukanin dalibai biyu da UTME da DE kan iya ziyarta shafin don duba ko sun sama gurbin karatu a Jami’ar Gwamnatin Taraya dake Wukari a Shafin intanet na JAMB CAPs.

Yadda Dalibai zasu duba ko FUWUKARI ta Basu gurbin karatu na shekarar 2020/2021 ?

Daliban su ziyarci www.jamb.gov.ng/efacility

Su shigar da adreshin Email din su tare da numbobin sirrin dasuka zaba yayin Rijista jarabawar JAMB na shekara 2020/2021.

Su latsa Kan “CHECK ADMISSION STATUS” bayan sun shiga cikin shafin.

Su danan “ACCESS JAMBCAPS” sai su danan kan ” check Admission status

Ko Kuma su sauke manhajar JAMB CAPS zuwa wayoyin su don duba wa dashi.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*