JAMB 2021: Za a Rufe Saida e-PIN Rijistan Jarabawar UTME/DE 10 ga Watan Mayu

Za’a Rufe rijista jarabawar JAMB na shekarar 2021/2022 a ranar 15 gawatan Mayu, 2021. Abinda dalibai da dama Basu sanni ba shine za arufe saida ePIN din rajistan jarabawar kafin ranar Rufe rijista baki daya. Hakikanin gaskiya, za’a rufe Saida e-PIN ranar 10 gawatan Mayu, 2021.

Wanan na nufi duk dalibin da bai malaki ePIN dinsa ba kafin ranar 10 ga watan Mayu, 2021. Ba zai Samu damar yin rijista jarabawar JAMB na shekarar 2021/2022, duk dacewa za’a rufe ranar rajistan jarabawar ne 15 gawatan Mayu, 2021.

Babu wanin cibiyar yin rajista da zata iya wa dalibai rajistan jarabawar ba batare da ePIN ba.

Adon haka muke shawarta dukan daliban dake son yin rajistan jarabawar JAMB na shekarar 2021/2022, cewa suyi kokari su malaki ePIN dinsu kafin ranar 10 ga watan Mayu, 2021.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*