Karin Kudi Makarata: Kan Shuwagabanin Dalibai Jami’ar Kaduna Nason Rabuwa

Tun bayan bayanan batun karin kudin Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), Shuwagabanin Dalibai ke ta Kai kawo wajen ganin Gwamnatin Jihar Kaduna ta duba lamarin don rage kudaden zuwa wanin adadi da daliban ka iya biya.

Wasu daga cikin Shugabanin dalibai sun aika da takardu ga sarakunan gargajiya, Malaman adinai, da masu ruwa da tsaki don sa baki alamuran, don ganin Gwamnatin Jihar Kaduna ta duba lamarin.

Sai dai bagaren guda wasu Shuwagabanin naganin bai kamata abi wanan hanyar ba don cinma mafita, sun kar kata ne akan cewa zanga zanga shine kadai mafita.

Sunce “ta hanyar zanga zangane kawai Gwamnati Jihar Kaduna zata saurari kukan su ama hanyar bibiyan wasu jami’ai don shiga lamarin bazai haifar da matsalaha bah.

Domin Kuwa ilimi haki ne ga duk yankasa kamar yada sakin layi baka na 18 , shafi na biyu na kudin tsarin mulki Nijeriya na shekara 1999 da aka yi wa kwaskwarima yabayana, ama ba Kasuwanci bah a cewar su”.

Sai dai wasu naganin hanyar zanga zanga ba zai haifar da da Mai ido ba, don aganin su haqan su ya kusan cima ruwa bazasu goyabayyan hakan ba har sai Gwamnatin ta ki amincewa da bukatun su sanan zasu tafi ga mataki nagaba.

Dukan ban garorin Shuwagabanin sun Fara Zargin junan su yayin da bangare dake son ayi zanga zanga ke tunanin Kamar an bai wa bangaren da basu so ne kudi don suyi shuru da bakinsu.

Kawone bangare na ta Kiran dalibai dayanayi bukutar su, kuma dukan bangarorin nada dalibai dasuke goya musu baya.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*