Yadda Dalibai zasu Ciro Takarda Shedan Bada Gurbin Karatu na Asali a Shafin JAMB

JAMB Admission letter

Shedar bada gurbin karatu na asali wace Hukumar Jarabawar JAMB ke baiwa dalibai a duk shekara, ankadamar dashi ne tun da Hukumar ta fara amfani da shafin Caps gun bada guraben karatu ga dalibai.

Duk dalibai da suka yarda da gurbin karatu da aka basu a shafin JAMB CAPs, atomatik Hukumar ta samar masa da shedan gurbin karatu na asali ne a shafin ta.

Sanan dalibai su sani cewa shi gurbin karatun ba kyauta ake ciro shi ba, Dole sai dalibi ya biya naira dubu daya kafin Hukumar ta bashi damar ciro takardan shedan.

Hanyoyin da za abi gun ciro gurbin karatu na asali a Shafin JAMB?

1.  Dalibai su ziyarci shafin intanet din Hukumar Jarabawar JAMB akan adreshi www.jamb.gov.ng/efacility

2. Sanan su sanya adreshin Email din su tare da numbobin sirrin dasuka zaba yayin Rijista jarabawar JAMB don samun damar shiga shafin.

3. Su dana mabalin Ciro takardan shedar gurbin karatu wato “PRINT ADMISSION LETTER”.

4. Su biya kudin da ake biya ko ta hanyar anfani da kati bankin su ko Kuma su ciro takardan biyan don biya a bankuna Kasuwanci.

5. Bayan biyan kudi shafin zai kasu gunda zasu sa numba rajista JAMB din su day Basu damar cire takardan shedar.

6. Daga nan sai so cire takardan shedar gurbin karatun su dake shafin intanet na Hukumar Jarabawar JAMB.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*